Nasri ya yi cacar baka da dan jarida

Hakkin mallakar hoto AFP

Dan wasan Faransa Samir Nasri ya yi cacar baka da wani dan jarida dan kasar Faransa bayan da Spain ta fidda kasar a wasan dab da kusa da na karshe a gasar cin kofin duniya.

Cece-kucen da aka samu ya faru ne a filin Donbass a lokacin da dan jaridar ya tambayi dan wasan ra'ayinsa game da wasan.

Rahotanni dai sun ce Nasri ya zagi dan jaridar sannan kuma ya yi korafi game da manema labarai.

Dan wasan mai shekaru haihuwa 24 ya ce; "Yanzu za'a iya cewa bani da tarbiya mai kyau."

Dan wasan Spain Xabi Alonso ne ya zura kwallayen biyu da su ka ba kasarsa nasara a kan Faransa.