'Yan wasa kamar ka: Gano dan wasa kamar ka da ma'aunin BBC Hausa

Yayinda ya rage kwanaki talatin a soma wasannin Olympics a birnin London, gidan radiyon BBC ya kaddamar da wani ma'auni akan shafukansa na internet wanda zai baiwa mai amfani da shafin damar gwada tsawo ko nauyinsa da na kowanne daga cikin 'yan wasan 1,800 da suka samu lambar girma a wasannin Olympics na shekara ta 2008 da aka yi a birnin Beijin.

An sanya jadawalin ne wanda aka sakawa suna athletes like you, watau 'yan wasa kamar kai, akan shafukan intanet na harsuna 15 daga cikin harsuna 27 da BBC ke watsa shirye-shiryenta a cikinsu.

Wannan sabuwar fasahar dai tana da kafar da mai amfani da ita zai iya saduwa da shafukan zumunta kamar su Facebook da Twitter.

Fasahar dai za ta kuma baiwa mai amfani da ita damar samun bayanai masu zurfi game da rayuwar kowanne dan wasa.

Editan riko na sashen Hausa na BBC Elhadj Coulibally ya ce gurbin na Athlete like you kari ne bisa ga salo iri daban-daban a fasahar intanet da gidan radiyon BBC ke fito da su a wani bangare na shirye-shiryen bayar da rahotanni game da wasannin na Olympics.