Sunderland za ta sanya jesi na Afrika

sunderland sponsor Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption sunderland sponsor

Kungiyar Sunderland da ke gasar Premier ta Ingila ta bayyana cewa ta kulla yarjejeniya da wani kamfani mai neman bunkasa harkokin kasuwanci a nahiyar Afrika da zai dauki nauyin rigar wasansu.

Kungiyar za ta sanya sunan kamfanin a jikin jesinta na tsawon akalla kakar wasanni biyu.

Kamfanin mai suna ''Invest in Africa'' hadakar kamfanoni ne daban daban da su ka hadu wuri guda domin bunkusa harkokin kasuwanci a Afrika ta hanyar zawarcin 'yan kasuwa masu zuba jari zuwa Afrika.

A shekarar da ta gabata kungiyar ta Sunderland ta kulla yarjejeniya da kungiyar kwallon kafa ta Asante Kotoko ta Ghana, inda Sunderland din ke taimakawa Asanten a fannin horo da shawarwari ga matasan 'yan wasanta.

Shugaban Sunderland Ellis Short ya yaba da yarjejeniyar da suka kulla da kanfanin ya na cewa su na alfahari da kulla dangantakar da kamfanin wadda za ta amfani yankinsu da kuma nahiyar Afrika, nahiyar da ta zamo wani ginshiki na nasarorin da kungiyar ta samu a baya bayan nan.