Jaridar Italiya ta nemi gafarar Balotelli.

mario balatelli Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mario Balotelli

Wata jaridar kasar Italia ta wasanni mai suna Gazetta dello Sport ta nemi gafara a kan wani zanen raha da tayi na dan wasan kwallon kafa na Italiya Mario Balotelli, da ta suranta shi da Kinko.

Wasu masu karanta jaridar sun yi korafi a kan zanen ,wanda ke nuna dan wasan a kan wani katan tsauni ya na ta buge kwallaye bayan kammala wasan Italiya da Ingila.

A sanarwar bada hakurin da jaridar ta fidda ta ce zanen ba ya daga cikin kyawawan zanen da kwararren mai zanen raharta ke yi. Jaridar ta ce ta wadanda su ke karanta ta ce a don haka idan wasu masu karanta ta ba su ji dadin zanen ba, tana basu hakuri.

Sai dai jaridar ta yi watsi da zargin danganta ta ko kuma mai zanen rahar nata, Valerio Marini, da nuna wariyar launin fata.

Sanarwar ta ce a wannan lokacin dole ne a rinka yin taka tsan-tsan da kuma baiwa mutane abin da yake da kyau saboda ana iya yiwa komai fassara ta daban.

Jaridar ta kara da cewa ita kanta tana yaki da duk wani nau'i na wariyar launin fata a kowana filin wasa kuma tana sukan ihun da ake yiwa Balotelli da cewa rashin sanin yakamata ne kuma kauyanci ne.

Dan wasan na Manchester City Balotelli, da dan asalin kasar Ghana ne yana fuskantar batanci na wariyar launin fata kusan a duk lokacin da yake bugawa Italiya wasa.

Kafin gasar cin kofin kasashen Turai ta Euro 2012,Balotelli ya ce zai fita daga filin wasa idan wani dan kallo ya ci masa mutunci. Zanen rahar dai ya jawo mummunan suka daga wata kungiya mai yaki da nuna bambamcin launin fata da ake kira Kick It Out.