Federer ya yi nasara zuwa zagaye na uku.

roger federer
Image caption Roger Federer

Na uku a jerin zakarun 'yan wasan tennis a duniya,Roger Federer ya yi nasara a kan abokin karawarsa a gasar Wimbledon wanda shi kuma ya ke matsayin na 68 a duniya, Fabio Fognini, dan Italiya da ci 6-1 6-3 6-2, da wannan nasara Federer ya sami damar zuwa zagaye na uku na gasar.

Federer wanda sau shida ya na lashe gasar ta Wimbledon ya sami nasarar zuwa zagaye na uku a gasar ta Wimbledon da a ke yi cikin sauki ba tare da gamuwa da wani babban kalubale daga abokin karawar tasa ba, inda ya ce ya ji dadin yadda ya yi wasan musamman ma yadda ya sami natsuwa.

Federer dai ya na fatan ganin ya sami nasarar lashe gasar ta Wimbledon a karo na bakwai domin ya zama dai dai Pete Sampras wanda ya taba lashe gasar ta Wimbledon har sau bakwai.

Yarima Charles tare da mai dakinsa Duchess of Cornwall ya je kallon wasan na Wimbledon a karon farko bayan shekaru 42, inda ya kalli karawa ta Federer da Fognini.