Kocin Masar yana harin zuwa gasar Kofin Duniya

bob bradley Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Bob Bradley

Bayan ya kasa tsallakewa da Masar, zuwa gasar cin kofin kwallon kafa na kasashen Afrika da za a yi a Afrika ta Kudu a shekara mai zuwa, kocin Masar yace burinsa shi ne ya kai kasar gasar cin Kofin Duniya da za a yi a Brazil, a shekara ta 2014.

Bob Bradley dan Amurka ya kasa tsallakewa da Masar din ce a wasan zagaye na biyu da Masar din ta yi da Jamhuriyar Afrika ta tsakiya, ranar Asabar,inda suka yi kunnen doki daya da daya wanda hakan ya baiwa Afrika ta tsakiyan damar fidda Masar din da ci 4 da 3, idan aka tara makinsu na karawar farko da ta biyun.

Wannan dai shi ne karo na biyu a jere da Masar wadda sau bakwai tana daukar kofin kasashen Afrikan ba zata je gasar cin kofin ba.

Kocin yace daman babban burinsa shi ne ya kai kasar gasar Kofin Duniya wanda kuma a yanzu Masar din ce ke kan gaba a rukunin da ta ke ciki.

Mr Bradley ya ce ba wai yana neman wanke kansa ba ne daga laifin kasa tsallakewa zuwa gasar cin Kofin kasasshen Afrikan ba ne.

Kocin wanda aka dauka aikin horadda 'yan wasan na Masar tun a watan Satumba na bara bai fara aiki ba sai a watan Yuni da ya gabata, yace ya karbi aikin ne a yanayi na tsaka mai wuya amma duk da haka sun yi kokarin zama jagaba a rukuninsu na zuwa gasar cin Kofin Duniya.

Mr Bradley ya kara da cewa juyin juya halin da aka yi a kasar ya jefa harkar kwallon kafa cikin wani hali baya ga rikicin da ya yi sanadin mutuwar sama da mutane saba'in a wani wasa a bara.