Spain da Italiya zasu kara a wasan karshe yau

'yan wasan spain da Italiya Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption 'yan wasan spain da Italiya

Spain da Italiya zasu kara a wasan karshe na cin kofin kwallon kafa na kasashen Turai, Euro 2012. Za a fara karawar ce da karfe bakwai da minti arba'in da biyar agogon Najeria, a babban birnin Ukraine, Kiev.

Idan Spain ta yi nasara akan Italiya zata shiga kundin tarihi a matsayin kasa ta farko da ta yi nasarar cin manyan gasar kwallon kafa uku a jere, kasancewar su zakarun gasar kwallon kafar ta Turai ta 2008 da kuma gasar Kofin Duniya na 2010.

Idan kuma Italiya ta sami nasara akan Spain zai zamo karo na biyu ke nan da ta ci kofin Turan tun bayan wanda ta ci a 1968,hakan kuma zai sa ta zamo nasara ta baya- bayan nan da ta samu tun 2006 da ta ci Kofin Duniya.

Wannan ita ce karawa ta 31 da kasashen za su yi a tarihi, inda Italiya ta yi galaba akan Spain din sau 10 ita kuma Spain din ta sami nasara akan Italiyan sau 8,sannan kuma sau 12 su na tashi canjaras.

Karin bayani