Spain ta sake daukan Kofin Turai

spanish players Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Spanish players celebrating

Kasar Spain ta lallasa Italiya da ci 4 ba ko daya ta sake daukan kofin kwallon kafa na kasashen Turai,Euro 2012 a birnin Kiev na Ukraine.

David Silva shi ne ya fara saka wa Spain kwallonta ta farko ana minti 14 da fara wasa sai Jordi Alba ya kara ta biyu a minti 41, yayin da Fernando Torres ya jefa ta uku ana mintina tamanin da hudu da wasan bayan wasu mintina hudu kuma sai Juan Mata ya jefa kwallo ta hudu kuma ta karshe aragar Italiya.

Da wannan nasara yanzu Spain ta zama kasa ta farko da ta sake daukan kofin na kasashen Turai sau biyu.

A karawar kasashen biyu Spain da Italiya sau talatin da daya a tarihi,Italiya ta sami nasara sau goma Spain kuma ta sami ta tara a yanzu , kuma sunyi canjaras sau goma sha biyu.

Haka kuma Spain din ta kafa tarihi yanzu da kasancewa kasar da tayi nasarar zama zakara a jere a jere sau uku a gasar da ta kunshi kasa da kasa.

Karin bayani