Kwadwo Asamoah na Ghana ya koma Juventus

kwadwo asamoah
Image caption Kwadwo Asamoah

Kungiyar Juventus ta tabbatar da cewa ta dauki dan wasan Ghana Kwadwo Asamoah. Dan wasan mai shekaru ashirin da uku, ya bi sahun dan kasar Chile Mauricio Isla wajen ficewa daga kungiyar Udinese zuwa Juventus din.

Da komawar tasa Juventus, Kwadwo zai zama na biyu a 'yan wasan Ghana da suka bugawa kungiyar ta Juventus wasa, bayan kyaftin din Ghanan Stephen Appiah, wanda ya bar kungiyar a shekara ta 2005.

Asamoah ya shedawa BBC cewa ya kulla yarjejeniyar shekara biyar da kulob din wanda sau ashirin da takwas ya na zama zakara a kasar Italiya..

Tun a watan da ya gabata ne aka yi wa Asamoah da Isla gwajin lafiyarsu amma ba a fidda bayanin kwantiragin nasu ba sai a ranar Litinin din nan.

Dukkanin 'yan wasan sun koma Juventus din bisa yarjejeniyar hadin guiwa, inda kungiyar za ta biya Euro miliyan tara na kashi hamsin cikin dari na rijistar Asamoah.

Karin bayani