Ingila ta zama ta hudu a duniya - FIFA

'yan wasan ingila Hakkin mallakar hoto
Image caption 'Yan wasan Ingila

Ingila ta zama ta hudu a duniya daga matsayi na shida a jerin kasashen hukumar kwallon kafa ta duniya,FIFA, duk da rashin nasarar da ta yi a wasan gab da na kusa da na karshe na cin kofin kasashen Turai da aka kammala.

Zakarun Turai kuma masu rike da Kofin Duniya Spain, sun cigaba da kasancewa a matsayi na daya yayin da Italiya wadda ta fitar da Ingila a bugun daga-kai-sai-mai-tsaron-gida a wasan na kasashen Turai, Euro 2012, ta matsa gaba da mataki shida inda ta zama ta shida a duniya.

Brazil mai masaukin gasar cin Kofin Duniya ta 2014 ta fice daga jerin kasashe goma da ke kan gaba a kwallon kafa a karon farko tun da aka bullo da tsarin auna kasashen a 1998,inda ta yo kasa da mataki biyar, ta zama ta goma sha daya yanzu.

Kasashen da aka fitar da su a wasan kusa da na karshe na Euro 2012, Jamus da Portugal sun cigaba, yayin da Jamus ta zama ta biyu, portugal ta zama ta biyar.

Koma bayan da Brazil wadda sau biyar ta na daukar Kofin Duniya ta samu a jerin kasashen bai rasa nasaba da rashin yin manyan wasanni a shekarar 2012 kamar sauran fitattun kasashe.

Ivory Coast wadda ta ke ta 16 a duniya ita ce ta daya a Afrika, sai Ghana ta 33 a duniya kuma ta biyu a Afrika, Algeria ta 3 a Afrika ta zama ta 35 a duniya, yayin da Najeriya ta matso daga ta sittin a duniya zuwa ta 58.

Karin bayani