Di Matteo yace ba ya fargaba akan Guardiola

roberto di matteo Hakkin mallakar hoto All Sport
Image caption Roberto Di Matteo

Kocin Chelsea Roberto Di matteo ya ce ba shi da wata fargaba a kan rade radin daukar tsohon kocin Barcelona Pep Guardiola na ya maye gurbinsa a kungiyar.

A watan da ya gabata ne dai a ka nada Di Matteo a matsayin kocin na Chelsea na dun-dun-dun bayan zaman rikon kwarya da ya yi, sakamkon nasarar da Chelsea ta yi ta daukar kofin Zakarun Turai da kuma Kofin Kalubale.

Kocin ya ce hankalinsa a kwance yake a kan aikinsa saboda yana da kwararrun 'yan wasa da kuma sababbi domin haka ba shi da wata fargaba a kakar wasanni mai zuwa.

Di Matteo ya ce tun lokacin da a ka nada shi cikakken kocin kungiyar ake ta rade radi a kansa saboda haka ba shi da wata fargaba ta cewa wani zai kawar da shi daga mukamin, zai cigaba da aikinsa matukar iyawarsa kuma ya rage ga kowa ya ce ko ya rubuta abin da yaga dama.

Karin bayani