An hana jami'an Najeriya halartar Olympics

Image caption Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan

Gwamnatin Najeriya ta ce ba za ta tura jami'anta kasar Burtaniya domin halartar gasar Oympics ba.

Za dai a fara wasan ne a watan Yuli a birnin London.

Ministan Harkokin Wasannin Mista Bolaji Abdullahi ya ce gwamnati ta dauki matakin ne da zummar rage kashe kudi ba-gaira-babu-dalili.

Kazalika ya ce rashin halartar jami'an gwamnatin zai sanya 'yan wasan da ke wakilartar Najeriya a gasar su fi mayar da hankali wajen wasanninsu.

Mista Bolaji Abdullahi ya kara da cewa a baya, jami'an gwamnatin da ba su da alaka da harkar wasanni sun sun halarci gasar Olympics kuma hakan wata asara ce.

Ministan ya ce duk gwamnan da ke son halartar gasar ta Olympics sai dai ya yi hakan da kudinsa, amma ba da kudin gwamnati ba.

Karin bayani