FIFA ta amince da fasahar tantance shigar kwallo raga

manuel neuer Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Manuel Neuer

Hukumar kwallon kafa ta duniya, FIFA,ta amince da amfani da fasahar zamani wajen tantance shigar kwallo raga a wasan kwallon kafa a kuri'ar da aka yi a taron majalisar hukumomin kwallon kafa na duniya, IFAB, ranar Alhamis din nan.

Kafin majalisar ta amince da yin amfani da tsarin, sai da aka gabatar da sakamakon jarraba fasahar da aka yi, domin sanin yadda ingancinta yake wajen kawo karshen matsalar da ake samu ta kasa tantance shigar kwallo raga da alkalan wasa kan gamu da ita a wasu lokuta.

Fasahar ta na da fannoni biyu ne, daya ya kunshi na'urorin daukar hoto guda shida da za a sa a kowaca raga, wadanda zasu rinka lura da kwallon duk inda ta ke a filin wasa, da zarar kwallon ta tsallaka layin bakin raga sai na'urorin su aika sako agogon alkalin wasa cewa kwallon ta shiga raga.

Daya fannin kuma ya kunshi wata 'yar na'ura ce da za a sanya a cikin kwallo wadda ke amfani da maganadisun kurar karfe a bakin layin raga inda da zarar kwallon ta tsallaka layin bakin ragar na'urar za ta nuna alamun bambamcin wurin da kwallon ta ke, kuma daga nan na'urar za ta aike da sako zuwa agogon alkalin wasa cikin kasa da dakika daya.

Kamar yadda hukumar kwallon kafa ta duniya, FIFA, ta tsara dukkanin sakwannin biyu za su kai ga agogon alkalin wasa cikin kasa da dakika daya, ta inda ba zai dauki wani dogon lokaci ba na tantancewa ko kwallon ta tsallaka layin ko ba ta tsallaka ba.

Za a fara amfani da tsarin a wasan cin Kofin Duniya na kungiyoyi da za a yi a watan Disamba a Japan.

Shugaba da kuma babban sakataren hukumar kwallon kafa na Ingila David Bernstein da Alex Horne sun je Zurich domin jefa kuri'arsu akan amfani da tsarin.

Hukumar kwallon kafa ta Ingila da ta Scotland da ta Wales da kuma ta yankin Arewacin Ireland su na da kuri'a dai dai da zasu jefa, yayin da hukumar kwallon kafa ta duniya ,FIFA ta ke da kuri'u hudu, kuma duk wata doka da za a sauya ta kwallon kafa sai ta sami rinjayen akalla shida daga cikin kuri'un takwas.

Karin bayani