Olympics: Neman gurbi uku na kwallon kwando

Lambobin yabon Gasar Olympics Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Lambobin yabon Gasar Olympics

Yayin da ya rage kasa da wata guda a fara Gasar Olympics, ga bayani na baya-bayan nan a kan ci gaban da 'yan wasan Afirka da ma sauran wurare suka samu:

Girka, da Lithuania, da Rasha sun shiga zagaye na karshe na wasan kwallon kwando bangaren maza a Venezuela, a yunkurinsu na samun gurabe uku na karshe a Gasar Olympics.

Duka kasashen uku dai sun samu kaiwa wannan mataki ne bayan sun yi nasara a matakin rukuni, ana kuma sa ran za su kai matakin wasan kusa da na karshe ranar Asabar.

Sai dai kuma Najeriya da Angola na fatan bayar da mamaki su kuma samawa kansu gurbi a Gasar ta Landan 2012.

A wasannin yau Najeriya za ta kara da Girka, Angola za ta fuskanci Rasha, Macedonia za ta kece raini da Jamhuriyar Dominican, sannan za a raba tsaki da tsakuwa tsakanin Lithuania da Puerto Rico.

Duk lokacin da aka yi tunani a kan gwarzayen Gasar Olympics, abin da ke zuwa zuciya shi ne 'yan wasan da suka samu lambobin yabo, ko suka yi fintinkau a duniya.

Amma a Tanzania, har yanzu John Stephen Akhwari gwarzo ne duk da cewa shi ya zo karshe a tseren ya-da-kanin-wani yayin Gasar Olympics ta 1968 a Mexico, saboda faduwar da ya yi, ya kuma yi mummunan rauni jim kadan bayan fara tseren.

Amma fa duk da haka bai karaya ba sai da ya dingisa ya isa filin wasan bayan sa'a daya da watsewar wadanda suka yi nasara, kafafuwansa jina-jina, daure da bandeji.

Da aka tambaye shi dalilin da ya sa bai hakura da tseren ba, sai ya ce: "Kasata ba ta tura ni don kawai in fara tseren ba; ta tura ni ne in kammala tseren".

Yanzu dai shekarun Akhwari da haihuwa saba'in da hudu, kuma yana zaune a kauyensa na asali a arewacin Tanzania.

To ko yaya ya ji a wancan lokacin da ya bayar da amsar tambayar da aka yi masa?

"To, a lokacin dai ni ban ji komai ba; sun tambaye ni kawai, ni kuma na ba su amsa. A lokacin na yi matukar gajiya", inji Akhwari.

Brazil ta bayyana sunayen dan wasan gaba na Porto, Hulk, da dan wasan baya na Real Madrid Marcelo, da kuma dan wasan tsakiya na AC Milan Thiago Silva a matsayin 'yan wasanta masu yawan shekaru da za su taka leda yayin Gasar Olympics ta Landan.

An kuma sanya sunayen mai tsaron baya na Manchester United Rafael da dan wasan gaba na Santos Neymar a cikin tawagar kasar mai mutane goma sha takwas.

Brazil dai na buri ne na samun lambarta ta farko ta kwallon kafa a Gasar Olympics. Tana kuma rukuni na uku tare da Masar, da Belarus, da kuma New Zealand.