Giggs ya zama kyaftin na Burtaniya

ryan giggs Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Ryan Giggs

Kocin 'yan wasan kwallon kafa na tawagar Burtania a gasar Olympics da za a yi a London Stuart Pearce ya nada dan wasan Manchester United Ryan Giggs a matsayin kyaftin din 'yan wasan su 18.

Kocin wanda 'yan wasan nasa za su kara da na Senegal a filin old Trafford ranar 26 ga watan Yuli, ya ce dukkanin 'yan wasan kungiyar suna mutunta Giggs.

Dan wasan mai shekaru 38, wanda yana daya daga cikin 'yan wasa uku da suka wuce shekara 23 da aka surka matasan 'yan wasan kwallon kafar na Burtaniya, ya ce ba karamin karamci ba ne nadin da aka yi ma sa.

Kocin tawagar ya ce yana ganin Giggs daban yake a cikin 'yan wasan, kuma shawarar nada shi kyaftin din ita ce hukunci mafi sauki da ya taba yi a tsawon aikinsa na kociya saboda dan wasan yana daya daga cikin kwararrun 'yan wasa a cikin shekaru 20 da su ka wuce.

Ryan Giggs wanda ya yi ritaya daga buga wasan kasa da kasa a shekara ta 2007, bai bugawa kasarsa Wales wasa ba saboda kasar ta kasa samun damar zuwa gasar cin Kofin Duniya ko na kasashen Turai a tsawon lokacin da ya ke wasa.

Bayan karawar tasu da Senegal, 'yan wasan na Burtaniya da ake yiwa lakabi da Team GB, za su fafata da Hadaddiyar Daular Larabawa a filin wasa na Wembley ranar 29 ga watan Yuli kafin daga karshe su kammala wasansu na rukuni da 'yan wasan Uruguay a filin wasa na Millennium ranar 1 ga watan Agusta.

Karin bayani