Suarez zai buga wasan Olympics

luis suarez Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Luis Suarez

Uruguay ta sanya sunan dan wasan Liverpool Luis Suarez cikin 'yan wasan kwallon kafa 18 da zasu buga wasan Olympics a London.

Dan wasan mai shekaru 25 na daga cikin 'yan wasa uku ma su yawan shekaru da suka hada da dan wasan Napoli Edinson Cavani da na kungiyar Palermo Egidio Arevalo Rios da aka surka su da matasan 'yan wasan kasar da zasu buga gasar Olympics.

Uruguay din ta kuma dauki takwaran Suarez din a kungiyar Liverpool, Sebastian Coates, da kuma dan wasan tsakiya na Ajax Nicolas Lodeiro a wadanda zasu yi mata wasan na Olympics.

Uruguay daya ce daga cikin kasashen da zasu kara da Burtaniya a rukunin farko, Group A, tare da Senegal da Hadaddiyar Daular Larabawa.

Uruguay wadda ta dauki kofin kasashen Latin Amurka da ya gabata kuma ta zo ta hudu a gasar cin Kofin Duniya na 2010 , ta na neman samun lambar gasar Olympic ce karo na uku, bayan da 'yan wasanta suka sami lambar zinariya a gasar Olympics ta 1924 a birnin Paris da kuma wadda suka kara samu shekaru 4 bayan nan a Amsterdam.

Karin bayani