Aboutrika zai yiwa Masar wasan Olympics

aboutrika Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mohamed Aboutrika

Dan wasan tsakiya na kungiyar Al Ahly kuma tshohon zakaran dan kwallon Afrika na shekara na BBC Mohamed Aboutrika na daya daga cikin 'yan wasa uku ma su yawan shekaru da zasu bugawa Masar wasan kwallon kafa na Olympics.

Sauran 'yan wasan biyu da kocin tawagar kwallon ta Masar Hany Ramzy ya zaba su ne Emad Moteab da Ahmed Fathi, wadanda su ma 'yan wasan kungiyar ce ta Al Ahly wadda sau shida ta na daukar kofin zakarun Afrika.

Sau goma sha uku ne dai Masar din ta na samun zuwa gasar kwallon kafar ta Olympics inda kasar ta zamo ta uku a gasar wasan 'yan kasa da shekaru 23 ta Afrika ta farko da aka yi a Morocco bara.

Sai dai wannan shi ne karo na goma sha daya da kasar ta shiga gasar bayan da ta kaurace mata a shekarun 1956 da 1980 sabo da dalilai na siyasa.

Karin bayani