Fitaccen dan wasa, Joe McBride ya mutu

Image caption Joe McBride

Joe McBride dan wasan gaba na kulob din Celtic da suka ci gasar wasan zakarun turai na shekarar 1967 ya mutu bayan ya yi fama da cutar shanyewar rabin jiki.

McBride yana cikin sanannun masu cin kwallo a tarihin Celtic.

Shugaban Kulob din Celtic, Peter Lawwel ya ce "Joe Mutumin kirki ne, salihi wanda kuma ya ba da babbar gudunmawa ga ci-gaban kulob din".

Ya kara da cewa: "za a yi kewarsa a kulob din. A madadin kowa a kulob din ina mika ta'aziyya ta ga iyalin sa."

Karin bayani