West Ham na son sayen Andy Carroll

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Andy Carroll

Daya daga cikin mutanen da suka mallaki kulab din West Ham, David Gold, ya ce suna son sayen dan wasan Liverpool, Andy Carroll, idan har kulab dinsa zai sayar da shi.

Sai dai ya ce ba a fara wata tattaunawa a kan batun ba.

Da ma dai ana ta yin tsokaci game da yiwuwar komawar Carrol West Ham tun bayan da sabon kocin Liverpool, Brendan Rodgers, ya ce za su iya bai wa West Ham aron dan wasan.

Mista Gold ya shaidawa BBC cewa: "ba mu yi wata tattaunawa a tsakaninmu(shugabannin kulob) ko kuma da Liverpool ba, game da sayen Andy Carroll. Amma hakan ba wai yana nufin ba mu da sha'awar sayensa ba ne idan kulob dinsa zai sayar da shi''.

Carroll ya bar kulob din Newcastle ya koma Liverpool a watan Janairun 2011 akan kudi fam miliyan 35, kuma ya zura kwallaye 11 a wasannin 56 da ya bugawa kulob din na Liverpool.

Karin bayani