Fletcher na fuskantar matsalar komowa wasa

darren fletcher Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Darren Fletcher

Dan wasan Manchester United Darren Fletcher na fuskantar gagarumin kalubale na ci gaba da wasa sabo da ciwon da yake fama da shi.

Sai dai kocin United Sir Alex Ferguson ya ce za a baiwa dan wasan na tsakiya damar sauya wurin da ya ke buga wasa a kungiyar idan bai sami saukin ciwon da yake damunsa ba.

Tun a watan Nuwamba ne Fletcher baya samun damar bugawa kungiyar wasa saboda matsalar ciwon gyambon ciki da yake fama da ita, amma yana fatan dawowa fagen wasa kafin kakar wasannin da za a shiga.

Tun a watan Nuwamba ne Fletcher dan shekara 28 ya buga wasansa na karshe lokacin da Manchester ta yi 2-2 da kungiyar Benfica a gasar Kofin Zakarun Turai.

Karin bayani