Rodallega ya koma Fulham

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption fulham sun dauki rodallega

Kulob din Fulham ya dau dan wasan gaba Hugo Rodallega dan yi masa wasa na tsawon shekaru uku. Dan wasan mai kimanin shekaru 26 da haihuwa,ya sanya hannu akan yarjejeniyar yiwa kulob din Fulham aiki na wani lokaci,inda a yanzu zai bar kulob din sa na Wigan zuwa wani lokaci. Kungiyoyi da dama ne suka bayyana shaawarsu na daukar wannan dan wasa. Manajan Fulham Martin Jol, ya bayyana farin cikinsa da daukar Rodallega,bayan da kulob din sa na Fulham bai yi nasarar samun dan wasan gaba Pavel Pogrebnyak ba wanda yanzu haka yake tare da kulob din Reading. Martin Jol yace ''Nayi farin cikin samun dan wasa kamar Rodallega, bisa la'akari da kwazon sa, da kuma yadda kungiyoyi da dama a Ingila ke rububin daukarsa,a saboda haka ina fata zai yi bakin kokarinsa wajen ganin kulob din Fulham ya kara daukaka'.