Owen na neman sabon kulob

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Micheal Owen

Dan wasar kungiyar Manchester United Michael owen ya bayyana cewar ya na jiran wata dama ce kafin kakar wasanni ta bana don komawa sabon kulob,amma ya ce ba zai je kungiyar wasar da ba ta kai rukumin gwanaye ba.

Tsohon dan wasan kwallon Ingilan dan shekara 32,ya nace a watan mayun nan kan cewar ba zai yi ritaya daga buga wasar kwallon kafa ba duk da barin kulob din Manchester da yayi bayan da ya buga musu wasanni har na tsawon shekaru uku a jere.

Sai dai a shafin sa na twitter Owen yace idan har wata babbar dama ba ta samu ba, ba wata matsala.

Amma yace ya san tabbas zai samu kyakkyawar dama domin ya sha nuna alamun hakan idan akayi duba da yadda yake buga wasa.

Karin bayani