An kebe wuraren da jiragen sama ba zasu bi ba a lokacin Olympics

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Wani sojan saman Burtaniya mai harbi daga boye ke jarraba dabarunsa na yaki a wajen da za a yi wasannin

A yayinda birnin London ke shirye shiryen karbar bakuncin wasannin Olympics nan da makonni biyu masu zuwa, an ware wasu yankuna da ba za a ketara da jirgin sama ba.

Idan wasannin suka kankama dai dakarun saman Birtaniya za su iya amfani da makamai idan jirgi ya shiga yankunan kuma ya ki biyayya ga gargadin cewa ya bar wurin.

Air Vice-Marshal Stuart Atha babban jamiin samar da tsaron sama a wasannin na Olypmpics Ya ce: '' za mu taimaka maka ka bar sararin samaniyar, idan kuwa ka ki amsa umurninmu, kuma ka cigaba da kin yin biyayyar, to ba mu da wani zabi face mu yi amfani da karfi a kanka''.

Wannan dai na daga cikin matakan tsaron birnin na London ke dauka gabanin wasannin na Olympics na shekara ta 2012

Karin bayani