Daukar Kofin Premier ne burinmu —Sir Alex

alex ferguson Hakkin mallakar hoto Getty

Kocin Manchester United Sir Alex Ferguson yace sake daukar Kofin Premier shi ne babban burinsu.

Yace dole ne mu sake farfadowa kamar yadda muka yi a lokuta da dama,wannan shi ne babban burinmu a wannan shekara, mu dawo da kofin.

Ferguson yace ''wannan wani muhimmin bangare ne a tarihinmu tsawon shekaru ashirin ko dai mu dauki kofin na Premier ko kuma mu zo na biyu''.

A tarihin kungiyar sau hudu ta na sake farfadowa ta dauki kofin na Premier bayan ta zama ta biyu a karshen gasar ta Premier karkashin jagorancin Sir Alex din, a shekarun 1996 da 1999 da 2007 da kuma 20011.

A cikin mako mai zuwa ne kuma Manchester United za ta je Afirka ta Kudu inda za ta yi wasannin sada zumunta

na share fagen kakar wasannin da za a shiga, inda za ta kara da kungiyar Amazulu da Ajax Cape Town kafin

kuma daga bisani ta tafi China ta fafata da kungiyar Shanghai Shenhua wadda Didier Drogba ya koma.A cikin

mako mai zuwa ne kuma Manchester United za ta je Afirka ta Kudu inda za ta yi wasannin sada zumunta na

share fagen kakar wasannin da za a shiga, inda za ta kara da kungiyar Amazulu da Ajax Cape Town kafin

kuma daga bisani ta tafi China ta fafata da kungiyar Shanghai Shenhua wadda Didier Drogba ya koma.

Karin bayani