Zamu ci gaba da kare kambunmu —Petr Cech

Petr Cech
Bayanan hoto,

Zamu cigaba da kare kambun mu.

Mai tsaron gida na kungiyar Chelsea Petr Cech yayi imani cewa za su kasance kungiyar kwallon kafa na farko da zata kare kambun ta na gasar Champions.

Ya jadadda cewa “zamu iya kalubalantar kowace kungiya a kakar wannan wasa kuma dole mu yi kokarin gain cewa mun yi nassarar lashe gasar champions a kakar wasani na biyu”

Da aka tambaye shi yadda za su cigaba da rike matsayin su a gasar Champions, ya jadadda cewa “babban kalubala ne, tunda ba wanda ya taba yin hakan zamu yi kokari muga mun yi hakan a karo na farko.”