Liverpool ba zata bayar da aron Carroll ba

andy carroll Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Andy Carroll

Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool tace ba zata bayar da aron dan wasan gaban ta Andy Carroll ba amma zata siyar da shi ga duk wata kungiyar da zata biya fan miliyan ashirin a kansa.

Kocin kulub din, Brendan Rogers ya ce za su duba yuwuwar sayar da dan wasan ga duk kungiyar da tayi tayin da ya dace.

Rodgers ya ce: "tunanin bada aron dan wasan da kungiyar ta kashe fam miliyan talatin a kansa ba abu ne da ke gaban su ba a wannan lokacin."

Rodgers ya kara da cewa, "Andy daya yake da kowane dan wasa a kulub din nan kuma zamu duba mu ga duk wani tayi da za a yi a kansa idan zai amfani kungiyar baki daya.

Kocin yace Carroll kwararren dan wasa ne. A mako mai zuwa zai dawo ya hadu da sauran 'yan kungiyar daga nan kuma sai mu duba mu ga abin da zai biyo baya.

Karin bayani