Liverpool ba za ta bayar da aron Andy Carroll ba

Liverpool Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Dan wasan Liverpool Andy Carroll

Liverpool ta ce ba za ta bayar da aron Andy Carrol ba, amma za ta sayar da dan wasan ga duk kungiyar da za ta biya fam miliyan 20 a kansa .

Kungiyar Newcastle na nazari akan mataki na gaba ,akan dan wasan me shekaru 23 bayan yunkurin farko da ta yi na karbar sa aro ya ci tura.

Sai dai kocin kulob din na Liverpool Brendan Rodgers ya ce , za su yi nazari kan duk wani tayi da akayi a kan dan wasan wanda ya dace.

Rodgers yace tunanin bada aron dan wasan da kungiyar ta kashe fam miliyan 30 a kansa ba abu ne da ke gabansu ba yanzu.

A watan Janairu na shekara ta 2011 aka sayarwa kungiyar Liverpool shahararen dan wasan , a kan fam miliyan 35, wanda ya kasance a matsayi na 3 na farashi mafi tsada na sayar da dan wasa a cikin kungiyoyin kwallon kafa a Burtaniya.

Karin bayani