Rafeal Nadal ya janye daga wasan Olympics

rafeal nadal Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Rafeal Nadal

Zakaran wasan Tennis na Olympics Rafael Nadal ya janye daga shiga gasar wasan Olympics yana cewa ba shi da koshin lafiyar da zai iya fafatawa.

Nadal dan shekara 26 yana fama da ciwon guiwa ne da yace ba zai iya kare lambar zinariyar da ya samu a gasar Olympics da akayi a birnin Beijin a 2008 ba.

Dan wasan tennis din ya ce ban sami kaina a yanayin da zan iya shiga gasar ba.wannan lokacin yana daya daga cikin lokuta na nadama a rayuwata ta wasan tennis.

Nadal na uku a fagen wasan tennis a duniya ya zama cikin zakarun wasan tennis biyar a duniya da suka sami lambar zinariya a wasan tennis na Olympics na 'yan wasa dai-dai lokacin da ya yi nasara akan Fernando Gonzalez dan Chile shekaru hudu da suka wuce a Beijin.

Karin bayani