Puyol ya dawo atisaye da Barcelona

carles puyol Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Carles Puyol

Dan wasan baya na kungiyar Barcelona Carles Puyol ya dawo atisaye bayan watanni biyu da aka yi masa aikin raunin da ya ji a gwiwa.

Nan da dan lokaci ake saran dan wasan zai dawo ya rika buga wasa sosai bayan jiyyar raunin da ya hana shi zuwa gasar cin Kofin Kasashen Turai, Euro 2012, da aka yi a Poland da Ukraine.

Puyol mai shekaru 34 ya ji raunin ne a dai-dai karshen kakar wasanni ta 2011-12.

Kyaftin din na Barcelona ya motsa jiki ba tare da sauran 'yan wasan kungiyar ba a atisayen da suka yi kafin na karshe Kafin tashinsu zuwa Jamus ranar Talata domin wasan sada zumunta na gwaji da kungiyar Hamburg.

A ranar Litinin mai zuwa za a sake duba Puyol domin a tantance ko zai iya dawowa cikakken atisaye ranar da 'yan wasan dake bugawa kungiyar Spaniya ta kasa wadanda suke kungiyar zasu dawo domin fara shirye shiryen tunkarar kakar wasannin da za a shiga.

Karin bayani