Arsene Wenger yana son Van Persie

arsene wenger
Image caption Arsene Wenger

Kocin Arsenal Arsene wenger yana son Robin van Persie ya cigaba da zama a kungiyar duk da cewa dan wasan ya bayyana aniyarsa ta tafiya inda ya ce ba zai sabunta kwantiraginsa da kulub din ba.

Kocin yana son a kawo karshen takaddamar da ake yi da dan wasan kafin kakar wasannin gasar Premier ta fara ranar 18 ga watan Agusta.

Arsene Wenger yace ''dan wasan yana da sauran shekara daya a kwantiraginsa kuma wadansu kungiyoyi suna bukatarsa amma burinmu shi ne mu cigaba da kasancewa tare da shi''

''Amma dai zamu yi abin da yafi amfani ga kungiyar. Idan kana da lura zaka ga haka'' inji Wenger

Van Persie ya ci kwallaye 37 a kakar wasannin da ta gabata 30 daga cikinsu a gasar Premier, ya kuma zama zakaran kungiyar kwararrun 'yan wasa da kungiyar marubuta wasanni na shekara.

Sai dai yadda kulub din ya zo na uku a karshen gasar Premier da ta wuce, dan wasan mai shekara 28 ya yi watsi da bukatar sabunta kwantiraginsa kuma yana tantama akan burin kungiyar.

Ranar 31 ga watan Agusta ce wa'adin dakatar da musayar 'yan wasa amma Wenger ya ce za su tsaida nasu lokacin na kawo karshen takkadama akan danwasan kafin zuwan wa'adin.