An bukaci dan tsallen Burtaniya ya ba da bayani

Phillips Idowu Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Dan wasan tsallen badake na Burtaniya, Phillips Idowu

Hukumar kula da gasannin Olympic ta Burtaniya (BOA) ta bukaci dan wasanta na tsallen badake, Phillips Idowu, ya mika mata bayani dangane da raunin da ya yi a cinya, al'amarin da ya hana shi halartar wani sansanin horo.

Dan wasan mai shekaru talatin da uku, wanda ake sa ran zai fafata a Gasar Olympics ta bana ranar 7 ga watan Agusta, bai je sansanin horar da 'yan wasan Burtaniya a Portugal ba.

Babban jami'in kula da lafiya na hukumar ta BOA, Dokta Ian McCurdie, ya rubuta takarda ga dan wasan, wadda a cikinta ya bukaci Idowu ya aike masa da bayanan lafiyarsa.

Sai dai kuma wakilin dan wasan tsallen, Jonathan Marks, ya ce wannan mataki na BOA ya ba shi takaici da mamaki.

A bana dai Idowu, mai fatan samun lambar zinare a gasar ta Olympics, ya shiga gasanni sau uku ne kacal.

Sannan kuma tun ranar 1 ga watan Yuni dan wasan, wanda ya samu lambar azurfa a Beijing shekaru hudu da suka gabata, bai sake shiga wata gasa ba.

Zakaran tsallen badaken na duniya na 2009 yana fadi-tashin ganin ya rike wuta, bayan ya yi tsallen mita 16.43 da mita 17.05, abin da ya gaza kaiwa matakin da ya saba na mita 17.81.

Karin bayani