Za a Rufe Portsmouth

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Stadium, Portsmouth

Kungiyar kwallon kafa ta Portsmouth ba ta da wani zabi illa da ta rufe kulab din goma ga watan Agusta; har sai dai in mayan 'yan wasa na kulab din sun amince su sauya kulab ko kuma a rage masu albashi.

Jami'in gudanarwa na kungiyar Trevor Birch ya ce "Babu wani boye boye dole ne 'yan wasan su bari kuma su karkare shirin barin kulab din."

Kungiyar magoya bayan Pompey da Portpin sun nuna sha'awar sayan kulab din amma a bisa ka'idar cewa za a rage masu albashi ta hanyar sayar da 'yan wasa da yarjejeniyar fahimtar juna.

"idan har ba mu nuna wani chigaba na musamman ba zuwa goma ga watan Agusta, ba mu da wani zabi illa mu rufe kungiyar."

Karin bayani