Zamu karo 'yan wasa - Inji Wenger

arsene wenger Hakkin mallakar hoto
Image caption Arsene Wenger

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya tabbatar da cewa kungiyar za ta kara sayen 'yan wasa kafin lokacin musayar 'yan wasa da ake ciki ya kare.

Bayanda aka ruwaito cewa Arsenal din na harin sayen dan wasan tsakiya na Malaga akan kudi fam miliyan 15.6, Wenger ya tabbatar da hakan amma ya kawar jita-jitar da ake yi ta cewa kungiyar za ta sayi dan wasan Rennes Yann M'vila.

Arsene Wenger wanda yake yiwa manema labarai jawabi a Beijin inda kungiyarsa za ta yi wasa da Manchester City ranar Juma'a da aka tambaye shi akan makomar Robin van Persie wanda ya ke son barin kulub din yace babu wani karin bayani da zai yi illa dai suna son cigaba da zama da 'yan wasansu, kuma zai yi farin ciki idan dan wasan ya tsaya.

Kungiyar ta Arsenal dai ta sami karin karfi da sayen Lukas Podolski da Olivier Giroud kuma wasu daga cikin 'yan wasanta da suke yi rauni sun warke.

Karin bayani