Usain Bolt ya murmure

Dan tseren Jamaica Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Usain Bolt

Dan tseren Jamaica Usain Bolt ya ce ya murmure daga raunin da ya ji kuma a shirye ya ke ya kare kambunsa a wasanin Olympics da za a bude yau a Landan .

Bolt ya lashi takobin kasancewa daya daga cikin taurarun da za su ja hankalin yan kallo a tseren mita 100 da 200.

“wannan shi ne lokacin da zan bude wani sabon babi a rayuwa ta.”Inji Bolt

Usain Bolt wanda shi ne ke rike da kambun tseren mita 100 da 200 ya sha kaye daga hanun abokin samun horo Yohan Blake a gwaje-gwajen da aka yi a Jamaica. Kuma tun bayan lokaci yake fama da ciwon baya da kuma raunin da ya ji a cinyarsa gabanin wasanin

Bolt wanda zai rike tutar Jamaica a bikin bude gasar Olympics ya nuna sha’awar sa ta daukan lambar gwal guda hudu a tseren mita 400 da na mita 100