BBC navigation

West Ham ta amince ta karbi aron Carroll

An sabunta: 31 ga Yuli, 2012 - An wallafa a 11:44 GMT
Andy Carroll dan wasan Liverpool

Dan wasan gaba na kulob din Liverpool, Andy Carroll

Kungiyar kwallon kafa ta West Ham da ta liverpool sun amince a kan kudi fam miliyan biyu don bada aron Andy Carroll ga West Ham.

Yarjejniyar wacce za ta shafe tsawon kakar wasanni, za ta iya kaiwa fam miliyan goma sha bakwai a karshe, muddin kulob din na West Ham ya kasance a cikin gasar Premier.

Sai dai ana tsammanin dan wasan mai shekaru 23, baya son barin kulob dinsa na Liverpool kwata-kwata.

Liverpool wanda ya kafa tarihi a lokacin da ya sayi Andy Carroll a kan kudi fam miliyan talatin da biyar a watan Janairun shekarar 2011, ya ki amincewa da tayin da kungiyar New Castle ta yi da fari na sayen Carroll.

Tun lokacin da ya koma kulob din Liverpool, Andy Carroll ya yi ta fadi ta shi, inda ya ci gwala-gwalai 11 a wasanni 56 da ya buga.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.