An haramtawa 'yan wasan badminton 8 wasa

'yan wasan badminton na china da indonesia da koriya ta kudu Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'yan wasan badminton na China da Indonesia da Koriya ta Kudu

Hukumar wasan Badminton ta duniya ta haramtawa wadansu 'yan wasa mata su takwas masu wasan bibbiyu cigaba da wasa a gasar Olympics saboda zarginsu da kin dagewa domin samun nasara.

'Yan wasan da wannan hukunci ya shafa sun hada da hudu daga Koriya ta Kudu da bibbiyu daga kasashen Indonesia da China.

Hukumar ta dauki matakin ne akan zarginsu da yunkurin kin samun nasara da gangan a gasar Olympics.

Wata sanarwa da hukumar ta fitar ta tabbatar da cewa yan wasan na kasar Korea ta Kudu da na kasar China da kuma na Indonesia, an tuhume su ne da rashin zage dantse don yin wasan.

An zargi yan wasan ne da kin dagewa a karawar ta su bayanda tuni suka tsallake zuwa zagaye na gaba don su fuskanci abokan karawa marassa karfi.

Kasashen Indonesia da Koriya ta kudu sun daukaka kara akan matakin kuma ana saran kafin wasan gab da na kusa da na karshe, wato quater final ranar Laraba.

Karin bayani