Demba zai cigaba da kasancewa a NewCastle

Dan wasan tsakiya na Newcastle, Demba Ba Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dan wasan tsakiya na kulob din Newcastle, Demba Ba

Dan wasan tsakiyar nan na Newcastle Demba Ba, zai cigaba da kasancewa a Newcastle bayan wa’adin zamansa a kulob din dake kunshe a kwantiraginsa ya kare.

Dan wasan dan kasar Senegal mai shekaru 27 ya nuna sha’awar cigaba da buga wa kulob din wasa.

Kuma kocin kungiyar, Alan Pardew ya nuna kwarin gwiwa wajen rike shi a kulob din domin ya cigaba da wasa.

An jima ana rade-radi dai game da makomar dan wasan bayan ranar 31 ga watan Yuli, wato karshen ranar zamansa a kungiyar.

Ba, ya kammala kakar wasanninsa ta farko a kulob din Newscastle a matsayin wanda ya fi kowa zura kwallo a raga a kungiyar, inda ya zura kwallaye goma sha shida a ragar abokan

karawarsu. wanda hakan ya sa ya wuce dan kasarsa, Senegal, Papiss Cisse da shi ma yake kungiyar wanda kuma ya dawo daga kungiyar Freiburg, da kwallaye uku