Demba zai cigaba da kasancewa a NewCastle

Dan wasan tsakiya na Newcastle, Demba Ba Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dan wasan tsakiya na kulob din Newcastle, Demba Ba

Dan wasan tsakiyar nan na Newcastle Demba Ba zai cigaba da kasancewa a Newcastle bayan wa’adin barinsa kulob din dake kunshe a kwantiraginsa ya kare.

Dan wasan dan kasar Senegal mai shekaru 27 ya nuna sha’awar cigaba da buga wa kulob din wasa.

Kuma manajan kungiyar, Alan Pardew ya nuna kwarin gwiwa wajen rike shi a kulob din domin ya cigaba da ayyukansa.

Sai dai an yi ta rade-radi game da makomar Ba bayan ranar 31 ga watan Yuli.

Da wa'adin ya kawo wa kulob din fam miliyan bakwai da rabi.

Ba ya kammala kakar wasanninsa na farko a kulob din Newscastle a matsayin wanda ya fi kowa zira kwallo, inda ya zura kwallaye goma sha shida a ragar abokan karawars.