Arsenal na sa ran sayen Cazorla

Dan wasan Malaga, Santi Cazorla Hakkin mallakar hoto
Image caption Dan wasan Malaga, Santi Cazorla

Kulob din kwallon kafa na Arsenal na tattaunawa game da yarjejeniyar sayen Santi Cazorla daga kulob din Malaga da kuma aron Nuri Sahin daga kulob din Real Madrid.

Komawar Cazorla dan kasar Spain mai shekaru 27 Arsenal na da sarkakkiya, saboda matsalolin kudi da Malagar ke fuskanta.

Amma a wannan makon ne ake sa ran za a duba lafiyar Cazorla.

Shi kuwa dan wasan kasar Turkiya Sahin Nuri mai shekaru 23, zai kasance a Arsenal a tsawon kakar wasanni, idan dan wasan da kulob dinsa sun cimma yarjejniya da Arsenal.

Sai dai har yanzu ba a sa ranar da za a duba lafiyar Sahin ba.

Arsenal na fatan ganin cewa za a cimma yarjejeniyoyin biyu gabannin fara kakar wasanni.

A ranar goma sha takwas ga watan Agusta ne kulob din na Arsenal zai yi wasa na farko tare da Sunderland a gida.