''Fitar da Afrika a gasar kwallon kafa abin takaici ne''

'yan wasan senegal Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'Yan wasan Senegal

Mataimakin kocin Senegal Aliou Cisse yace fitar da kasarsa da Masar da akayi daga gasar wasan Olympics babban abin takaici ne ga wasan kwallon kafa a Afrika.

Yace ya dauki hakan a matsayin sheda ta cewa akwai bukatar daukar matakan aiki sosai domin rage gibin da ya ke tsakanin wasan kwallon kafa a Afrika da kuma sauran nahiyoyi.

Kafin ranar Asabar Senegal da Masar su kadai ne suka rage a kasashen dake wakiltar nahiyar Afrika a gasar ta Olympics amma su duka kuma suka yi rashin nasara inda Mexico ta yi galaba akan Senegal a karin lokaci da ci 4-2, yayin da Japan ta lallasa Masar da ci 3-0.

Suma kasashen da suka wakilci nahiyar Afrika a kwallon kafa ta mata a wasan na Olympics Kamaru da Arika ta kudu ba su sami damar wuce zagayen wasan rukuni-rukuni ba kuma koda wasa daya ba su ci ba.

Mataimakin Kocin na Senegal yace babu shakka idan aka duba irin nasarar da Afrika ta samu a gasar Olympics din a Kwallon kafa a baya, gasar 2012 ba karamin koma baya ba ta zama ba.

Najeriya wadda a Afrika ta fara daukar lambar zinariya ta wasan kwallon kafa na Olympics a Atlanta a 1996 ta sami damar zuwa wasan karshe a gasar Olympics da ta gabata a Beijin inda ta yi rashin nasara a karshe a karawarta da Argentina a 2008.

Karin bayani