Olympics: Birtaniya ta samu lambobin zinari 6 a rana daya

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Wasu magoya bayan tawagar Birtaniya a wasannin Olympics na London

Birtaniya tana shagulgulan samun nasararda bata taba samu ba a rana daya a gasar wasannin Olympics tun fiye da shekaru dari da suka gabata.

Tawagar wasan kasar sun ci lambobin zinari shidda a fagen wasannin motsa jiki da tseren keke da ninkaya ranar assabar.

Baki daya dai an cinye lambobin zinariya ashirin da biyar a ranar da aka kira wata rana mai alfarma ta assabar.

Mo Farah, wanda ya je Brittaniya a matsayin dan gudun hijira daga Somalia ya ci lambar zinariya a tseren mita dubu goma, ya bayyana ta a matsayin ranar da ya fi samun farin ciki a rayuwar sa.

Oscar Pistorius wani gurgu dan Afrika ta Kudu da aka yi ma kafafun karfe ya zo na biyu a tseren mita dari hudu inda yace: ''Na ma rasa abinda zan yi, in yi kuka ne don murna, ko ko nace kai a'a akwai wani aiki a gaba na."

Karin bayani