Kungiyar Arsenal ta sayi Cazorla

Hakkin mallakar hoto
Image caption Santi Cazorla

Kungiyar Arsenal ta sayi dan wasan tsakiya na Malaga, Santi Cazorla, bayan da aka tabbatar da koshin lafiyarsa.

Carzorla ya shiga kulob din ne a lokacin da suke atisaye na gabanin kakar wasan bana a sansanin horar da 'yan wasansu a Jamus.

Dan wasan mai shekaru 27, wanda dan kasar Spain ne, ya sanya hannu a kwantiragi da kulob din na tsawon lokaci a kan kudin da ake gani bai kai fan miliyan goma sha biyar ba

Matsalar karancin kudi da Malaga ke fama da ita ta sa aka samu jinkiri wajen komawarsa Arsenal din tun da farko.

A gefe guda kuma, Arsenal na tattaunawa domin aron dan wasan tsakiya na kulob din Real Madrid, Nuri Sahin.

Shugabannin kulob din na fatan samun wadannan 'yan wasan zai kara wa kulob din tagomashi bayan dan wasan gaba na Jamus, Lukas Podolski da kuma dan wasan tsakiya na Faransa, Olivier Giroud sun koma kulob din.

Karin bayani