Ingila ta cigaba a jerin kasashen FIFA

'yan wasan ingila Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption 'Yan wasan Ingila

Ingila ta kai matsayi na 3 inda ta shige gaban Uruguay wadda ta dauki kofin kwallon kafa na kasashen Latin America, gasar da FIFA ta daina la'akari da ita wajen auna karfin kasashen.

Kasar Wales ta karu da matsayi daya inda ta zamo ta 37 daga 38, Scotland kuma ta cigaba sosai daga ta 49 zuwa ta 46 sai kuma Ireland ta Arewa ta karu da matsayi daya zuwa ta 101.

Jamhuriyar Ireland kuwa wadda ba ta sami nasara ba a dukkanin wasannin rukuni uku na gasar Euro 2012 ta cigaba da kasance wa a matsayinta na 26.

A ko wana wata ne Hukumar Wasan kwallon Kafa ta Duniya, FIFA, ta ke fidda matsayin kasashen ta hanyar auna yawan wasanni masu muhimmaci da kuma tsanani da kowace kasa ta yi bisa la'akari da karfin abokanan karawa.

Zakarun Turai da Duniya Spain sun cigaba da rike matsayinsu na daya yayin da Jamus iata ma ta ci gaba da zama ta biyu.

Zakarun duniya sau biyar, Brazil da zasu karbi bakuncin gasar cin Kofin Duniya ta 2014 sun cigaba da samun koma baya da a yanzu suka ruftu zuwa matsayi na 13 da bata taba zuwa ba.

Brazil ta sami wannan koma baya ne saboda bata yi wasu wasanni masu yawa ba da wasu kasashe da su ke da karfi a wasan kwallon kafa a wannan shekara ta 2012 kamar sauran kasashen da suke kan gaba a jerin jadawalin.

Faransa ta na matsayi na 14 Chile ta na na 15 sai kuma Ivory Coast a matsayi na 16 amma ta daya a Afrika.

Ghana ta na matsayi na 32 a duniya amma ita ce ta 2 a Afrika yayin da Aljeriya ta sami matsayi na 34 a duniya ta sami matsayi na 3 a Afrika.

Najeriya wadda ta ke mataki na 58 a duniya ita ce ta 11 a Afrika Kamaru tana bi mata a duniya a matsayi na 59 a Afrika ma tana bayanta a matsayi na 12

Karin bayani