Semenya ta yi nasarar zuwa tseren kusa da na karshe

caster semenya Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Caster Semenya

Tsohuwar ta daya a gasar tseren mita 800 a duniya 'yar kasar Afrika ta Kudu Caster Semenya ta sami nasarar zuwa tseren kusa da na karshe a shigarta ta farko gasar Olympics.

'Yar tseren mai shekara 21 wadda aka duba ta domin tantance jinsinta bayan da ta sami nasara a Gasar Wasannin guje-guje da tsalle-tsalle ta 2009 ta Duniya ta sami cancantar shiga tseren kusa da na karshen inda ta kammala tseren a cikin mintina 2 da dakika 00.71.

'yar tseren Birtaniya Lynsey Sharp da ta Amurka Alysia Johnson Montano da kuma ta Kenya mai rike da kambun gasar Pamela Jelimo dukkanninsu sun sami tsallakewa zuwa wasan kusa da na karshen.

Sarah Attar 'yar wasan tsere ta farko ta kasar Saudi Arabia itace ta zo ta karshe, amma duk da haka 'yan kallo sun yi mata tafi sosai bayan da ta kammala tseren da dakika 43 tsakaninta da wadda ta zo ta daya Janeth Jepkosgei Busienei 'yar Kenya wadda ita kuma ta kammala gudun cikin 2:01.04.

Labarin Caster Semenya ya bazu ne a duniya bayanda ta ci gasar Duniya a 2009, inda aka bukaci da ayi mata binciken kwakwaf domin tantance jinsinta ganin yadda ta zage da gudun da kuma yadda kirar jikinta take kamar ta namiji.

Hukumar wasannin guje-guje da tsalle-tsalle da motsa jiki ta Duniya ta dakatar da ita tsawon watanni 11 a lokacin amma daga baya aka wanke ta daga tuhumar zargin zama namijin kuma ta dawo fagen tseren a watan Yuli na 2010.

Duk da ciwon baya da take fama da shi a watan Yulin na 2010 ta sami nasarar daukar lambar azurfa a gasar tsere ta Duniya a lokacin a Daegu.

Karin bayani