Kungiyar Lille ta baiwa Maccabi aron Enyeama

vincent enyeama
Image caption Vincent Enyeama

Kungiyar kwallon kafa ta Lille dake Faransa ta bada aron maitsaron gidanta kuma na Najeriya Vincent Enyeama zuwa kulob din Maccabi Tel-Aviv na kasar Israela.

Dan wasan mai shekara 29 ya koma kulob din Lille ne a kakar wasannin bara amma bai sami sa'ar zuwa kungiyar ba saboda sau uku kacal aka sa shi a wasa.

Enyeama shi ne na biyu dake zaman mataimakin mai tsaron gidan kungiyar ta Lille, tsohon mai tsaron gidan Faransa Mickael Landreau amma kwatsam sai kocin kulob din Rudi Garcia ya kawo wani maitsaron gidan Steeve Elana abin da zai kai ga gogayyar neman matsayi a tsakanin masu tsaron gidan uku a kakar wasanni mai zuwa in badon yanzu da aka bada aron Enyeaman ba .

A wani lokaci a baya Enyeama ya taba yiwa kungiyar Hapoel Tel-Aviv wadda su ke gari daya da kungiyar Maccabi wasa.

Karin bayani