An haramtawa dan Korea ta Kudu lambar yabo

Wasan kwallon kafa tsakanin Korea ta Kudu da Japan Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Wasan kwallon kafa tsakanin Korea ta Kudu da Japan

An haramta wa wani dan wasan kwallon kafa na Korea ta Kudu karbar lambar yabonsa ta Olympics bayan an bayar da rahoton cewa ya daga wani sako na siyasa yayin karawar tawagarsa da ta Japan a wasan neman matsayi na uku a Gasar ta Olympics ta London.

An dai ce kyallen da dan wasan ya daga ya ambaci takaddamar da aka jima ana yi tsakanin kasashen biyu ne a kan tsibiran da ake kira Dokdo a Korea ta Kudu ko kuma Takeshima a Japan.

Dan wasan dai ya daga kyallen ne yayin wasan da tawagarsa ta lashe sa'o'i bayan shugaban kasar Korea ta Kudu ya kai ziyarar ba-zata tsibiran.

Kwamitin shirya Gasar Olympics na Duniya ya ce ya bukaci Korea ta Kudu ta dauki mataki nan take ta kuma yi masa karin bayani.

Karin bayani