City ta ci Chelsea ta dauki Garkuwar fara Premier

'yan wasan city na murna Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption 'Yan wasan City na murna

Manchester City ta lallasa Chelsea da ci 3-2 ta dauki Garkuwar wasan share fagen gasar Premier (Community Shield) a filin wasa na Villa Park.

Fernado Torres ne ya fara jefa kwallo a ragar City ana minti 40 da wasa amma bayan da ka dawo daga hutun rabin lokaci ana minti 53 sai Yaya Toure ya ramawa City bayan minti uku kacal sai kuma Tevez ya jefawa City kwallo ta biyu daga nan kuma mintina 6 tsakani sai Nasri ya ci kwallo ta uku.

Bayan da City din ta sami nasarar jefa kwallaye uku a ragar Chelsea a cikin mintina 12 a rabin lokacin ana minti 80 da wasa sai Bertrand ya ciwa Chelsea kwallo ta biyu.

Ana yin wasan daukar Garkuwar share fagen gasar Premier ne mako daya kafin fara kakar wasannin Premier, hakan na nufin a ranar Asabar 18 ga watan nan na Agusta za a fara gasar Premier ta bana.

Karin bayani