Brazil ta dora alhakin rashin nasararta a kan Rafael

dan wasan brazil Hakkin mallakar hoto xx
Image caption Dan wasan Brazil

Bayanda Brazil ta sha kashi a hannun Mexico a wasan karshe na gasar Olympics na kwallon kafa hukumar kula da harkokin kwallon kafa ta kasar ta yi abin da bata taba yi ba inda ta dora alhakin rashin nasarar a kan dan wasan kasar na baya Rafael wanda kuma dan Manchester United ne.

Hukumar a shafinta na yada bayanai na Intanet ta ware Rafeal mai shekara 21 ta dora masa alhakin wannan rashin nasara inda tace ''Rafeal ya sani cewa shi ne ya yi kuskuren bada kwallon da ta baiwa 'yan Mexico damar saka kwallonsu ta farko a wasan na karshe na gasar Olympics ta London ta 2012''

Sai dai hukumar ta kara da cewa ana samun kuskure ne domin a gyara a kiyayi gaba,tace ''Rafeal ya san haka kuma nan gaba idan al'amura suka lafa ba shakka zai duba yaga kuskurensa ya kuma gyara''.

To amma su kuma sauran 'yan wasa da masu basu horo matsayinsu a kan lamarin ya sha bam-bam domin galibinsu sun kare dan wasan ne.

Kocin nasu Mano Menezes yace Brazil tana da mintina 89 da zata rama cin da Mexicon ta yi mata amma bata iya ramawa ba, shi kuwa dan wasan gaba na Brazil din Neymar cewa yayi kowana dan wasa daga cikinsu har da shi kansa yana da laifi a rashin nasarar da suka yi. Mexico da ta ci Brazil 2-1 ne ta ci lambar yabo ta zinari a wasan. Brazil wadda sau biyar ta na daukar Kofin Duniya har yanzu bata taba zam zakara a wasan kwallon kafa na Olympics ba.

Karin bayani