An kwace lambar zinaren 'yar wasan Belarus ta Olympics

nadzeya ostapchuk Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Nadzeya Ostapchuk

Wata 'yar wasannin Olympics daga Belarus ta rasa lambar yabon zinaren data samu a wasannin , bayan gwajin da akai mata na amfani da kwayoyi.

'Yar wasannin Olympics din mai suna Nadzeya Ostapchuk, ita ce 'yar wasannin guje- guje da tsalle tsalle ta farko data rasa lambar yabon a wasannin Olympics na London na shekara ta 2012.

Bayan anyi gwajin fitsarinta ne dai, aka gano cewar tayi amfani da wasu abubuwa dake kara kuzari.

A yanzu dai, za a baiwa Valery Adams 'yar Kasar New Zeland lambar yabon tata.

An bada wannan sanarwa ne yayinda 'yan wasannin ke komawa Kasashen su.

Karin bayani