BBC navigation

Bin Hammam zai kalubalanci zargin FIFA na bannar kudade

An sabunta: 14 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 16:55 GMT
mohammed bin hammam

Mohammed Bin Hammam

Tsohon shugaban hukumar kwallon kafa ta Asia Mohammed Bin Hammam ya lashi takobin yin duk abin da zai iya domin wanke kansa daga zargin almubazzaranci da kudade da Hukumar kwallon Kafa ta Duniya FIFA, ta bullo da shi bayan da ta fara wani bincike a kansa lokacin da yake shugabancin hukumar ta Asia.

A wata wasika da ya aikawa 'yan kwamitin Hukumar Kwallon Kafar ta Asia Bin Hammam ya ce tuni lauyoyinsa suka maida martani akan matakin hukumar ta Asia da FIFA akan abinda ya ce wata kutinguila ce ta siyasa kawai.

Ya kara da cewa nan gaba kadan zai bayyana karin matakan da zai dauka na kalubalantar wannan keta doka da ka'ida da FIFA dinya ce ta yi.

Rahoton wani bincike na kwanan da aka yi a harkokin kudade na hukumar kwallon kafa ta Asia ya nuna yadda aka rinka biyan wasu kudade daban daban ga wasu daidaikun mutane,sai dai a martaninsa Bin Hammam ya bada dalilan yin hakan kuma ya nua cewa daga asusun ajiyarsa ne na kansa ya biya kudaden.

An zargi Bin Hammam wanda ya taba takarar shugabancin FIFA inda ya kalubalanci Sepp Blatter da yunkurin sayen kur'a kafin zaben shugabancin FIFA na bara.

A kan zargin FIFA ta haramta masa shiga duk wata sabga ta kwallon kafa a mtakin kasa ko duniya har tsawon rayuwarsa.

Sai dai a watan Yuli da ya wuce kotun sauraren kararrakin wasanni ta rushe wannan hyukunci inda ta ce babu sheadr da ta tabbatar da zargin da FIFA ta yi masa.

Amma duk da haka FIFA ta dakatar da shi tsawon kwanaki 90 wanda ya kara tsawon hukuncin dakatar da shi na kwanaki 30 da Hukumar kwallon kafa ta Asia ta yi masa.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.